Header Ads

Header ADS

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Likitar da ke kula da lafiyar iyalin Buhari ta rasu


Likitar Iyalan Buhari, Dr Marliyya Zayyana, ta rigamu gidan gaskiya
- Buhari ya ce sun dade tare da Likitar kuma ya yi babban rashi
- Shugaban kasa ya siffanta Likitar a matsayin mace mai mutunci yayinda ya aika sakon ta'aziyyarsa
Shugaba Muhammadu Buhari na jimami sakamakon rasuwar Likitar Iyalinsa, Dr Marliyya Zayyana.
Ta kasance tsohuwar shugaban Majalisar dattawan jami'ar gwamnatin tarayya dake Dutsinma, jijar Kastina.
A sakon ta'aziyyar da mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya saki, ya bayyana jimamin Buhari, NAN ta ruwaito.

A cewarsa, ta kasance kwararriyar Likita kuma mai mutunci wacce ta aiwatar da ayyukan kwarai a jami'an FUDMA.
"Rasuwarta na da ban jimami saboda ta kasance Likitar Iyalina kuma bugu da kari dan uwanta, Dr Suhayb Rafindadi, Likitana ne," Buhari yace.
Likitar iyalin Buhari, Marliyya Zayyana ta rasu, ya aika sakon ta'aziyya
Likitar iyalin Buhari, Marliyya Zayyana ta rasu, ya aika sakon ta'aziyya
Shugaba Buhari ya yi rashin manyan abokai da mukarrabai a wannan shekara.
Tsohon shugaban ma'aikatan fadarsa, Abba Kyari, ya rasa rayuwarsa bayan jinyar cutar Korona. Ya rasu ranar 17 ga Afrilu yana mai shekaru 67 a duniya.
Yan kwanaki bayan rasuwarsa, dogarin Buhari, Lawal mato, ya mutu bayan shekaru uku yana fama da ciwon siga.
A watan Mayu kuwa, Buhari yayi rashin dan'uwansa, Alhaji Ibrahim Dauda, bayan rashin lafiyan da yayi a Daura, jihar Katsina.
A watan Yuli, babban aboki kuma aminin Buhari, Mallam Isa Funtua ya rasu.

No comments

Powered by Blogger.