Header Ads

Header ADS

Gwamnatin Buhari ta sake yiwa 'yan Najeriya alkawari


Shugaba Buhari zai fitar da hanyar ragewa yan Najeriya radadin tashin farashin man fetur
- An kara farashin litan mai daga N148 zuwa N162 a watan Satumba
- Shugaba Buhari ya ce Najeriya ba zata sake biyan kudin tallafin mai ba
Gwamnatin tarayya a ranar Juma'a ta bayyana cewa ta kammala shirin raba motoci 2000 domin sufuri a fadin tarayya domin rage radadin tashin farashin man fetur kan yan Najeriya musamman masu zama a karkara.
Ministan harkoki na musamman, George Akume, ya bayyana hakan a Abuja a taron tattaunawar da yayi da yan kungiyoyin hadaka.
A cewarsa, shirin zai gudana ne tsakanin ma'aikatarsa, ma'aikatar aikin noma da raya karkara da kuma wasu hukumomin gwamnati.

Akume ya ce an yanke shawarar bi ta hannun kungiyoyin hadaka ne saboda tabbatar da aiwatar da shirin, maimakon baiwa wasu daidaikun mutane bashi, wanda hakan zai jinkirta aiwatar da aikin.
"Abinda muka lura shine, idan aka baiwa daidaikun mutane bashi, dawowa da shi na matukar wuya, amma idan akayi da kungiyoyin hadaka, abin zai fi saukin lura." Akume yace
"Manufar wannan shiri shine tabbatar da cewa mutanen karkara na samun saukin sufuri, yanzu da aka samu tashin farashin man fetur."
"Muna sane da cewa wasu yan kasuwan motocin haya zasu kara farashin hawa mota."
"Amma idan muka aiwatar da wannan shiri, mun yi imanin cewa zai rage tashin farashin don jin dadin al'ummarmu."
Ya ce babu yadda kasar nan zata cigaba ba tare da Sufuri ba wanda shine dalilin da yasa shugaba Muhammadu Buhari ke aiki tukuru ta bangaren gyaran hanyoyi, jiragen kasa da na sama.

Zamu rabawa yan sabbin dogayen motocin sufuri 2000 domin rage radadin hauhawar farashin mai - Gwamnatin Buhari
Gwamnatin Buhari
A bangare guda,  ta ce daga yanzu babu ruwanta da maganar tsayar da farashin mai, magana ta koma hannun 'yan kasuwa.
Jaridar Punch ta rawaito cewa babban sakataren hukumar PPRA, Abdulkadir Saidu, ne ya sanar da hakan.
A cewar jaridar Punch, Saidu ya bayyana cewa daga yanzu kayyade farashin litar mai zai dogara ne a kan bukatarsa da kuma farashin danyen mai a kauwar duniya.
Hakan na nufin gwamnati ta tsame hannunta daga tsayarwa ko kayyade farashin litar mai.
Tura wannan labari zuwa WhatsApp

No comments

Powered by Blogger.