Header Ads

Header ADS

Za a koma makaranta ranar litinin


Sakamakon bullar wannan cuta ta COVID-19, ya sanya harkar ilmin Najeriya da ma sauran kasashen duniya tabarbarewa, domin mafi yawan makarantu suna kulle, kuma su Kansu yaran sun gaji da zaman gida kamar yadda muka yi hira da su,

To sai dai ana cikin haka, jihar Legas ta ba da sanarwar cewa, za a koma makaranta 3 ga watan Agusta na wannan shekarar 2020,

To sai dai ba kowa da kowa ne zai koma makarantar ba, kawai daliban sakandare aji 6 da kuma aji 3 ne zasu koma domin rubuta jarrabawarsu ta karshe,

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa, bayan tattaunawa da suka yi da hukumomin kiwon lafiya daban daban, yanzu sun shirya tsaf domin komawa makaranta gobe litinin amma aji 6 da kuma aji 3 na sakandare kawai,

Sannan gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga gwamnatin tarayya kada a mayar da sauran baya, a fito da wani tsari wanda zai bai wa kowane dalibi zuwa ajin gaba ba tare da samun matsala ba.

No comments

Powered by Blogger.