Header Ads

Header ADS

Yanzu yanzu wata kungiya ta sace mutane masu dimbin yawa a jihar Borno


Wasu da ake zargin 'yan kungiyar ta'addanci ta Islamic State of West Africa Province (ISWAP) ne sun sace daruruwan mutane sunyi garkuwa da su a jihar Borno kamar yadda AFP ta ruwaito. 

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan masu alaka da kungiyar, a daren jiya Talata sun kai hari a Kukawa da ke Tafkin Chadi inda suka sace mutane masu yawa da suka dawo gidajensu bayan shafe shakaru biyu a sansanin yan gudun hijira a cewar Babakura Kolo, shugaban yan sa kai na yankin. 

A watan Yuni, a kalla sojoji 20 da farar hula fiye da 40 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wasu hare hare biyu da 'yan kungiyar suka kai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 

Kazalika, yan kungiyar ta'addancin sun kashe a kalla mutum 81 a wani hari da suka kai a wani kauye da ke karamar hukumar Gobiyo a jihar Borno a watannin baya. 

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇
https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9
Latsa nan domin biyo mu a shafin Twitter:👇
http://twitter.com/JaridarTalaka

Tura wannan labarin

No comments

Powered by Blogger.