Header Ads

Header ADS

Wata sabuwa: Naziru sarkin waka ya gaya ma gwamnan Kaduna wata magana mai ban mamaki


Tauraron mawakin Hausa kuma Jarumi, Nazir Ahmad Sarkin Waka ya mayarwa da Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai martani kan maganar da yayi na cewa kada dan Arewa ya fito neman takarar shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamna El-Rufa’i ya bayyana hakane a hirar da bBC ta yi dashi wanda yace dalili shine haka tsarin kasar yake bawai shima dan yana so ba.

Wannan ra’ayi na gwamnan Kaduna ya jawo martani da yawa tsakanin al'ummar Najeriya.

Nazir da yake mayar da Martani kan wannan magana ta shafinsa na Instagram ya bayyana cewa, “Wannan ra’ayinka ne kai da wanda basu san me na kasa ke ciki ba”

No comments

Powered by Blogger.