Header Ads

Header ADS

Wani gwamnan PDP ya cire sarakuna 12 daga mukamansu saboda sun kaiwa Buhari ziyara


Obiano ya dakatar da masu sarautar gargajiya 12 a jihar sakamakon ziyarar da suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a makon da ya gabata. Ya dakatar da wani basarake mai suna Igwe Peter Uyanwa, a kan zarginsa da yake da kai korafi daga yankinsa.

 Ya kara da janye shaidar amincewa ta basaraken. Dakatarwar ta shekara daya da aka yi wa masu sarautar, kamar yadda takardar ta ce, an yi ta ne saboda ziyarar da suka kai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tare da izininsa ba ko amincewarsa. 

An sanar da dakatarwar ne ta wata wasika da aka tura ga masarautun gargajiyar da ke fadin jihar Anambra, mai kwanan wata 11 ga Augusta, Gwamnonin arewa sun yi martani a kan zarginsu da hannu a Boko Haram Masu sarautar da abun ya shafa sune: Igwe Alex Edozieuno na Mkpunando; Igwe Mark Anthony Okonkwo na Alor; Igwe Chukuwma Bob Vincent Orji na Ezinifite; Igwe Engr G.B.C Mbakwe na Abacha;

 Igwe Chijioke Nwankwo na Nawfia and Igwe Nkeli Nelly na Igbariam. Sauran sun hada da: Igwe Anthony Onyekwere na Owelle; Igwe A. N Onwuneme na Ikenga; Igwe Simon Ikechukwu Chidubem na Umumbo; Igwe S. O Uche na Ezira; Igwe Dr Emeka Ilouno na Ifitedunu da Igwe Peter Ikegbunem Udoji na Eziagulu Otu. 

Wasikar dakatarwa an tura ta ne ga Obi na Onitsha, Alfred Achebe, wanda shine shugaban majalisar sarakunan jihar Anambra, kwamsihinan 'yan sanda da kuma daraktan hukumar jami'an tsaro ta farin kaya. Obiano ya ja kunnensu da su daina bayyana kansu a matsayin sarakunan gargajiya kuma su gujewa bayyana a hakan a yankinsu. Takardar ta bayyana kwace matsayinsu na 'yan majalisar sarakuna ta jihar tare da soke wasikar daukarsu aiki daga gwamnatin jihar. Gwamnatin ta kara da cewa, za a iya dage dakatarwar zuwa karshen shekarar nan, a sabunta ta ko kuma kara ta, duk hakan ya dogara ne da yadda suka ci gaba da al'amuransu. Amma kuma, uku daga cikin masu sarautar gargajiyar sun kwatanta hukuncin gwamnatin da abun takaici. 

No comments

Powered by Blogger.