Header Ads

Header ADS

Tsohon sarkin Kano zai koma makaranta~Karanta cikakken labarin a nan


Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na biyu zai koma jami’ar Oxford ta Ingila domin yin nazari da kuma bincike a cibiyar nazarin harkokin Afrika na jami’ar.
Rahotanni sun bayyana cewa zai soma bincikenne daga shekarar karatu ta bana watau daga watan Oktoban shekara ta 2020 zuwa 2021.
Cibiyar wacce ke jami’ar Oxford ta yi suna sosai wajen yaye dalibai a duniya wadanda ke rike da manyan mukamai a fannoni da dama.
Cibiyar ta nuna cewa Sanusi wanda shi ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, zai rubuta littafi kan yadda Babban bankin Najeriya ya shawo kan matsalar koma bayan tattalin arziki da ya shafi duniya daga shekara ta 2009 zuwa 2013.

No comments

Powered by Blogger.