Header Ads

Header ADS

To fa! Mata sun fusata akan maganar da jarumin shirin dadin kowa na tashar Arewa24 ya yi ~ Dantanin mai shayi


DUK mai kallon shirin diramar 'Daɗin Kowa' na gidan talbijin na Arewa24 ya san Ɗantani Maishayi, musamman yadda su ke gudanar da harkar su da Sallau a matsayin yaro da ubangida.
 
Shin wanene Ɗantani? Wakilin mu ya tattauna da Murtala Alasan, wanda shi ne ke taka wannan rol ɗin a cikin shirin, don ya fayyace mana tarihin rayuwar sa da yadda aka yi ya zama ɗan wasa, da sauran su.
 
 
FIM: Da farko za mu so ka gabatar da kan ka ga masu karatun mu.
 
MURTALA ALASAN: To, ni dai suna na Murtala Alasan, wanda a shirin 'Daɗin Kowa' aka san ni da Ɗantani Maishayi, sannan a wasan daɓe da mu ke yi aka san ni da Karabiti. 
 
Ni haifaffen unguwar Birget ne a cikin garin Kano; a nan aka haife ni a 1984. Kuma tun ina ƙarami iyaye na su ka taso su ka koma unguwar Badawa da zama. A nan na girma na yi makarantar firamare na yi sakandare. Kuma tun daga nan ne harkar dirama ta shiga zuciya ta, tun mu na yin na makaranta har wani lokaci, ba na mantawa, Ɗalha Musa Dakata, wanda a dirama ake kiran sa da Ɗanɗano, su ka kawo mana ƙungiyar dirama a nan unguwar mu. To, ta nan aka fara koya mini wasan daɓe, kuma har na samu sunan Karabiti.
 
To haka dai mu ka yi ta ci gaba, ƙungiyar mu ta na haɓaka. To daga nan dai har mu ka fara fitowa a fim.
 
Ba zan manta ba, fim ɗin da na fara fatowa a cikin sa shi ne 'Ɗan'adam Butulu', inda na fito a matsayin maigadi. To daga nan dai likkafa ta ci gaba, sai wani ya ɗauke ni mu ka tafi Abuja mu ke yi a can. To mu na can sai Allah ya kai Umar Kanu, sun je tare da Fati Muhammad, kuma da man da yake mun san juna da ita, saboda mun yi fim tare, don haka sai Umar Kanu ya ce, "To ai kai bai kamata ka zauna a nan ba, ka zo kawai mu tafi." Ya na kawo ni Kano sai ya haɗa ni da Ali Jita, a lokacin ma bai shahara ba, ya ce mu rinƙa aiki tare. Don haka kusan a harkar fim kowa da Ali Jita ya san ni, don ba ni da wani maigida sama da shi har yanzu.
 
To daga nan sai ya zama ina shiga wasu ayyuka na fim da mutane su ke yi; su kan ba ni aiki na bayan kyamara, har ma ya zama a kan ba ni sin ɗaya ko biyu, sai kuma a rinƙa cewa abin da na yi ya burge jama'a, ni kuma abin ya na ƙara shiga zuciya ta. 
 
To ana nan sai wani lokaci Nazir Adam Saleh ya kira ni ya ce, "Ga shi wani fim za a fara mai dogon zango, kuma ana son ka fito a matsayin mai shayi."  Kuma da na gwada aka ce ya yi. A lokacin ma ba Umar Jigirya ba ne a matsayin Sallau, wani ne daban, sai daga baya ya samu damar shiga matsayin Sallau. To a lokacin da aka fara ba na gari, kuma ban ma san muhimmancin abin ba, don haka sai aka yi ta kira na a waya, ina gobe zan dawo, jibi zan dawo, har ma aka ce a cire ni. Amma da Allah ya sa ina da rabo sai daraktan ya yi ta ba ni lokaci har dai na dawo. Kuma da yake ta nan Allah ya yi duniya za ta san ni, ka ga duk waccan gwagwarmaya da aka sha a baya sai ta zama tarihi, a yanzu duk inda na je a duniya ana kallo na ana kira na. Don haka babu abin da zan ce sai godiya ga Allah.
 
FIM: Kafin Wannan shirin na 'Daɗin Kowa' ko ka taɓa yin sana'ar shayi?
 
MURTALA ALASAN: Gaskiya a rayuwa ta ban taɓa yin sana'ar shayi ba, ban ma san yadda ake yin ta ba. Amma dai da aka ɗora ni a wannan rol ɗin da kuma yadda na ga ana karrama ni, sai abin ya ƙara shiga zuciya ta, har ta kai ta kawo sai na je na zauna a wajen mai shayi don na ga yadda ya ke mu'amalar sa da masu sayen shayin sa, sai na rinƙa yin amfani da shi a cikin shirin 'Daɗin Kowa'.
 
FIM: A cikin shirin, an fi sanin ka da yaron ka Sallau. Ko ya ka ke ganin yadda ku ke fafatawa?
 
Murtala Alasan a matsayin Ɗantani Maishayi a cikin shirin 'Daɗin Kowa'
 
MURTALA ALASAN: To ka ga dai tun a farko Sallau da shi da Ɗalha su ne su ka koya mini dirama, yau kuma sai ya zama a cikin 'Daɗin Kowa' ni ne maigidan sa. To gaskiya na ji daɗi don idan za mu yi aiki ya na fitowa a matsayin yaro, ni kuma maigidan sa, amma idan mu ka sauka daga fim ɗin kuma shi ne maigida na. Kuma gaskiya ina jin daɗin kasancewar mu da shi, don idan ya ga wani waje ban yi daidai ba ya kan gyara mini. To ka ga ƙauna ce, kuma ina jin daɗin wannan sosai.
 
FIM: Da yake ka yi suna a duniya, ko yaya ka ke kasancewa idan ka je wani gari?
 
MURTALA ALASAN: To gaskiya duk inda na shiga a faɗin duniya - don na shiga ƙasashe da garuruwa da dama, don ban taɓa zaton haka na ke da suna ba a duniya sai da wata tafiya ta shigar da ni Nijar; wallahi irin jama'ar da na gani, abin sai da ya tsorata ni, kuma duk inda na je ana ɗauka ta mai shayi. 
 
Kuma wannan tambayar da ka yi mini ta cewar ina shayi, haka mutane su ke yi mini a duk inda na je, kuma a yanayi irin namu babu irin jama'ar da ba ma haɗuwa da su: zaurawan ne 'yanmatan ne, wanda kuma a nan mu na samun ƙalubale wanda dole mu ke yin taka-tsantsan da kuma bi a hankali; kowa ya ce ya na son ka! To mace sama da dubu kowacce ta ce ta na so ta aure ka, yaya za ka yi da su? Ka ga dole sai ana yin taka-tsantsan! Kuma su matan ya kamata dai su rinƙa yi mana uziri.
 
FIM: Da yake ka na da iyali, ko daga cikin masoyan ka ne na shirin 'Daɗin Kowa' ka samu ka aura?
 
MURTALA ALASAN: To gaskiya ba daga cikin su ba ne, domin ita wadda na aura Allah ne ya yi ma 
zan aure ta, domin ni da man tun da na taso zan iya kiran kai na matsoraci a wajen mata. Don a yadda mu ka taso an yi Islamiyya a unguwa na je wajen 'yar wani in ba auren ta zan yi ba sai na ga ai yaudara ce, don haka ko da na taso ban saba da zuwa zance ba. Don haka matar da na aura zuwa zancen da na yi har mu ka yi aure bai kai goma ba. Don haka ba ta dalilin 'Daɗin Kowa' mu ka haɗu ba.
 
FIM: Da alamar nan gaba in za ka ƙara aure, a cikin masoyan da ka yi ne za ka yi ƙari.
 
Murtala Alasan ya sha gwagwarmaya a rayuwa kafin tauraruwar sa ta haska a cikin 'Daɗin Kowa'
 
MURTALA ALASAN: E to,  gaskiya akwai yiwuwar haka ɗin, domin a yanzu ba ni da tunanin zan zauna da mace ɗaya, don haka duk wadda Allah ya zaɓa mini tagari, in-sha Allah a shirye na ke.
 
FIM: Menene saƙon ka na ƙarshe?
 
MURTALA ALASAN: Saƙo na na ƙarshe shi ne ina godiya ga jama'a da su ke ƙauna ta, kuma ni ma ina ƙaunar su. Allah ya bar zumunci tare da mu.

Tura wannan labarin

No comments

Powered by Blogger.