Header Ads

Header ADS

To fa! Ko me ya yi zafi majalisa za ta gayyaci Buhari? ~ Karanta dalili a nan


'Yan majalisa a Najeriya za su gayyaci shugaba Muhammadu Buhari domin ya zo ya gaya musu dalilin da ya hana wasu daga cikin ma'aikatansa da ake zargi kan aikata ba daidai ba amsa gayyatar majalisa,

Majalisar wakilai ta yi barazana ga shugaban kasa domin ya zo ya gurfana a gabanta sannan ya gaya mata dalilin kin amsa gayyata da wasu manyan ma'aikatansa suka yi, ya yin da ake tuhumar su da aikata ba daidai ba,

Babban kwamitin da ke kula da asusun kudin gwamnati na majalisar ya ce, shugabannin  ma'aikatar CBN, NNPC, NPA, sun ki su amsa gayyatar da majalisar wakilai ta yi musu,

Kwamitin majalisar ya kara da cewa, akwai wadansu harkokin kudi ne wadanda ba a yi su akan ka'ida ba, sannan sauran ma'aikatu su ma suna da nasu matsaloli na rashin bin ka'ida, saboda haka dole su zo su amsa tambayoyi,


Wole Oke, shi ne shugaban kwamitin da ke kula da asusun kudin gwamnati na majalisar wakilai, kuma ya bayyana bacin ransa akan kin amsa gayyatar shugabannin wadannan ma'aikatu,

Kuma ya ce a gaggauta sanar da shugaba Muhammadu Buhari halin da ake ciki domin ya tursasa musu zuwa majalisar don amsa wadansu tambayoyi.

Source: JARIDAR RARIYA

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.