Header Ads

Header ADS

To fa! gwamnan jihar Kebbi ya yi wata zazzafar magana ~ Atiku Bagudu


Gwamnan jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya Abubakar Atiku Bagudu ya ce duk da cewa ana bincike kan musabbabin dalilin da ya sa aka ɗaure yaron nan a turken awaki, amma ya ce abin takaici ne irin wannan abin yana faruwa.
"Ƴan sanda ba su bani rahoto na su matan guda uku da ke gidan da uban yaron suka faɗa ba, amma abu ne na baƙin ciki kuma mai tayar da hankali," inji gwamnan.
Sai dai ya ce an ɗauki matakai na kulawa da yaron, inda ya gode dukkan waɗanda ya ce sun taimaka wajen ganowa da taimakawa kamar hukumar kula da 'ƴancin dan Adam da matarsa Zainab Bagudu da ma'aikatan gwamnati musamman na asibiti domin ƙoƙarin da suke yi na ba yaron kula ta musamman.
"Ina miƙa godiya ta ga ƴan jarida da suka fito da labarin fili, domin ba abin kunya ba ne, abin takaici ne. Gara al'umma ta farga cewa akwai abubuwa na assha da suna iya faruwa kuma ba mu sani ba."
Da BBC ta tambayi Gwamna Bagudu ko gwamnatinsa za ta sauya manufofinta ko kuma ta kafa wasu dokoki ganin yadda lamarin ya ja hankalin al'umma, sai ya ce wannan batun ya tabbatar da abin da ake cewa kowa yana da haƙƙi kan abubuwan da ke wakana a gidajen maƙwabta da unguwanni.
Ya ce: "Ina ƙara jawo hankalin al'umma cewa muna da haƙƙi. Ko ba a dora wa kowa laifi ba, lallai muna da haƙƙi ga maƙwabta kuma muna da haƙƙi da shiga da fita da ake yi a unguwanninmu. Muna da haƙƙi ga yaranmu ko ba mu muka haife su ba."
Ya kuma ƙara da cewa, "Akwai doka ta kare haƙƙin yara da inganta rayuwarsu da ke gaban majalisar jihar Kebbi a yanzu, kuma bi iznillah na san za a ƙara aiki a kanta sannan na san zan sa ma ta hannu.."
Gwamnan ya ce sabuwar dokar za ta faɗaɗa nauyin da ya rataya a wuyan gwamnati wajen karewa da kulawa da ƙananan yara ta ɓangaren lafiyarsu. Ya kuma tabbatar cewa dokar za ta tsananta hukunci kan waɗanda aka samu da laifin cin zarafin ƙananan yara a faɗin jihar.

No comments

Powered by Blogger.