Header Ads

Header ADS

To fa: Gwamnan jihar jigawa ya shiga masallaci tare da takalminsa inda ya yi raddi zuwa ga masu caccakar shugaba BuhariGwamnan jihar Jigawa, Gwamna Abubakar Badaru, ya kwatanta masu caccakar Buhari da masu gurbatacciyar zuciya da kuma rashin kishin kasa - Ya tabbatar da cewa an samu manyan nasarori tare da ci gaba masu tarin yawa a Najeriya sakamakon mulkin shugaba Buhari - Gwamnan ya kalubalanci jama'a da su duba nasarorin mulkin Buhari tare da alakanta shi da na gwamnatin da ta gabata .

Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar na jihar Jigawa, ya kwatanta masu kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari da masu gurbatacciyar zuciya da kuma rashin kishin kasa. A yayin jawabi a taron mambobin APC na kafafen sada zumuntar zamani na yankin arewa maso yamma da aka yi a Dutse, gwamnan ya ce halin da tsaron kasar nan ke ciki ya gyaru. Ba a hada yanzu da lokacin da ba, da mayakan ta'addanci na Boko Haram ke kai wa jama'a hari a wuraren bauta, kasuwanni, tashoshin mota da sauran wurare, 

Shafin Linda Ikeji ya wallafa. Badaru ya kara da cewa, a yanayin ayyukan inganta rayuwa da gwamnatin Buhari ta yi, za a iya cewa ya cika alkawurran da ya daukarwa 'yan Najeriya. Ya kalubanci 'yan Najeriya da su fito su duba nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu, sannan a alakanta su da na gwamnatin da ta gabata. Masu caccakar Buhari basu kishin Najeriya - Gwamna Badaru. Hoto daga shafin Linda Ikeji's Blog.
Source: Twitter.

Tura wannan labari zuwa:
WhatsApp da 
Twitter๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

No comments

Powered by Blogger.