Header Ads

Header ADS

To fa! Goodluck Jonathan ya yi magana mai zafi zuwa ga 'yan siyasar Najeriya


Tsohon Shugaban kasar Nijeriya Goodluck Jonathan ya gargadi ‘Yan siyasar kasar da su kaucewa duk wani yunkurin da zai haifar da tashin hankali, yayin da ya roke su da su rungumi hanyar inganta zaman lafiya da cigaban kasa.
Jonathan dake jawabi ga taron shugabannin Yan kabilar sa ta Ijaw yace ya zama wajibi Yan siyasa su sanya cigaban kasa a gaba, domin kuwa abinda siyasa ke bukata kenan amma ba raba kan jama’a ko kuma yaki da abokan gaba ba.

Tsohon shugaban yace a matsayinsa na mai fafutukar ganin dimokiradiya da shugabanci na gari ya wanzu a Nijeriya da Afirka, bukatar sa itace ganin jama’ar sa sun taka gagarumar rawa wajen zabin wanda zai jagoran ce su da kuma yadda ake jagorancin.

Jonathan yace babu abinda dake mayar da al’umma ko kasa baya da ya wuce tashin hankali da kuma rikicin shugabanci, inda ya kara da cewar babu yadda za suyi ikrarin son jama’ar su a daidai lokacin da suke amfani da damar domin cimma biyan bukatun kansu.
Tsohon shugaban ya bukaci hadin kan jama’ar Najeriya da kuma kaunar juna wajen kulla kawance daga kowanne sashe domin fuskantar kalubalen da suka addabi jama’a a wannan lokaci.
Jonathan yace ya zama wajibi yan Nijeriya su fahimci cewar makomar kasar da nasarar ta ya dogara ne ga hadin kan kasa daga matakai daban daban.
Tsohon shugaban ya kalubalanci shugabannin Yan kabilar sa ta Ijaw da su kulla kawance da sauran kabilun Nijeriya domin cimma muradun su.

No comments

Powered by Blogger.