Header Ads

Header ADS

Subhanallah! Wata mata ta kashe 'ya'yanta guda biyu (2) karanta a nan domin sanin dalili


Wata mata a kasar Ghana mai suna Abigail Agbubla Tetteh dake zaune a Sabon garin Tema, ta kashe 'ya'yanta biyu sakamakon bata da abinci da kuma kudin da za ta kula dasu,

Wannan matar dai a cikin zuciyarta ta dade da wannan mummunar dabi'a, domin ta bayyana cewa mahaifinsu baya kula da dawainiyarsu ko kadan,

Ita kuma ba wani karfin daukar dawainiyarsu take dashi ba, saboda haka hanya mafi sauki shi ne ta raba su da wannan duniya,

Abigail dai ta kashe 'ya'yanta guda biyu ne ta hanyar basu maganin bera, wanda hakan shi ne sanadiyar ajalinsu,

Bayan kwana daya da mutuwar yaran ne dai asirinta ya tonu, domin yaran suna cikin dakinta har tsawon kwana daya babu rayuwa a jikinsu, bincike da mutane suka yi na rashin ganin yaran har na tsawon kwana daya ne ya tona asirinta,

A lokacin da ake mata tambayoyi, Abigail ta bayyana cewa mijinta ya gudu kuma ya bar ta da lalurar yaran, ita kuma ba za ta iya daukar nauyin ciyar da su ba, saboda haka ta yanke hukuncin aika su lahira ta hanyar ba su maganin bera.

Source: Rariya Jarida

No comments

Powered by Blogger.