Header Ads

Header ADS

Shugaba Buhari ya siyo jirgin yaki daga kasar Rasha~Karanta abinda za a yi dashi


Jirgin dakon kaya na kasar Rasha ya sauka lafiya a wani sansanin sojojin sama dake Makurdin jihar Benue a tarayyar  Najeriya,

Jirgin dakon kayan ya sauke wani jirgin yaki mai saukar ungulu na zamani kuma kirar Mi-28NE wanda shi ne jirgin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya siyo daga kasar rasha domin yakar 'yan ta'adda,

Wannan jirgin yanzu haka babu irinsa a Najeriya wajen tsada, kyau, gudu, da kuma sauri wajen kai hare - hare ga 'yan ta'adda,

Tun ba yau ba dai, shugaba Muhammadu Buhari yana ikrarin cewa, zai yi maganin 'yan ta'adda a Najeriya, domin wannan na daga cikin kudororinsa da yake son aiwatar wa,

Abinda kowa ya sani ne, kasar Najeriya na cikin wani irin hali na miyagun 'yan ta'adda daban~daban a sassan Najeriya, to sai dai gwamnatin tarayya da sauran gwamnatoci sun ce suna iya bakin kokarinsu wajen ganin cewa an kawadda ayyukan ta'addanci a duk fadin Najeriya,

Wannan jirgi da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta siyo daga kasar Rasha, muna fatar za su yi amfani dashi kamar yadda ya dace, in ji DATTI ASSALAFIY.

source: RARIYA

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:
                      👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.