Header Ads

Header ADS

Sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa tsohon shugaban kasa Obasanjo ya fito


Sakamakon gwajin cutar korona na tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito bayan ya yi martani a kan mutuwar tsohon sanata Buruji Kashamu. Sakamkon ya bayyana dai baya dauke da cutar toshewar numfashin. A wata takarda da Kehinde Akinyemi, 

mataimakinsa na musamman a fannin yada labarai ya fitar, ya ce an yi gwajin a ranar Juma'a, 7 ga watan Augustan 2020. An yi gwajin ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke gidansa na Pent House, Okemosan, Abeokuta, a babban birnin jihar Ogun. 

Kamar yadda takardar da Akinyemi ya fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, ya ce Dr Olukunle Oluwasemowo ne ya dauki samfur din kuma yayi gwajin da ya dawo babu cutar a ranar Asabar, gwajin na daya daga cikin dakunan gwajin da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta aminta da su don gwajin cutar korona," takardar tace. 

Legit.ng ta ruwaito cewa, tsohon shugaban kasa Obasanjo a ranar Asabar, 8 ga watan Augusta, ya mika takardar ta'aziiyarsa ga gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, a kan mutuwar Sanata Buruji Kashamu. 

 Awasikar mai kwanan wata Asabar, 8 ga Augusta, tsohon shugaban kasar ya bayyana mutuwar Kashamu a matsayin rashin da ba za a iya mayar da shi ba. Yace: "Rayuwa da tarihin mamacin ya barmu da darrusa da dama." "Sanata Esho Jinadu (Buruji Kashamu) a rayuwarsa yayi amfani da lauyoyi da siyasa wajen sullubewa doka kan laifukan da aka zargin ya aikata a Najeriya da wajen Najeriya. Amma babu wani wayon lauyoyi, siyasa, al'ada ko ma na likitoci da ya hana mutuwar riskarsa lokacin da mahallici yace lokaci ya yi." Sai dai kuma da yake martani kan jawabin Obasanjo, Fayose, yace maganar Obasanjo abin kunya ne. "Abin takaici ne abinda Obasanjo yake fadi kan Buruji Kashamu bayan mutuwarsa don ya san ba zai iya ramawa ba. Me yasa bai fadi hakan lokacin da Kashamu ke raye ba?" Fayose ya ce. 

No comments

Powered by Blogger.