Header Ads

Header ADS

Ministan shari'a zai taimaka wa al'ummar jihar Kebbi game da shirin daukar ma'aikatan N - Power Batch "C"


A wani yunkuri wajen ganin cewa bai bar mutanen jiharsa a baya ba, ministan shari'a kuma attorney general a tarayyar Najeriya, Barrister Abubakar Chika Malami (SAN), ya fito da wadansu hanyoyi da zai taimaka wa duk wani dan asalin jihar Kebbi da ya cika shirin N - Power a wannan shekara,

Barrister Abubakar Chika Malami ya fito da wadansu hanyoyi da duk wani dan asalin jihar Kebbi zai ci moriyar wannan taimakon, ya yi hakan ne domin baiwa kowa damar samun wannan taimakon, hakan yana nuni da cewa Abubakar Chika Malami (SAN) Yana son kowa da kowa ya kasance ya shiga cikin wannan taimakon,

Hanyoyin da mutum zai bi domin samun taimako sun hada da:

1. Portal
2. Forms

1. Portal na nufin idan ka cika N-Power sannan kuma ka mallaki Slip dinka, zaka ziyarci wannan shafin domin tura bayananka da ake bukata game da N- Power, Abubakar Chika Malami (SAN), yana da website dinsa wanda a nan zaka je domin tura mishi bayananka na N~Power, wannan website din har tallarsa aka bayar a gidan rediyon jihar Kebbi, wato "KEBBI RADIO" domin ana bukatar duk wani dan asalin jihar Kebbi ya ziyarci wannan website din domin tura bayanansa na N ~ Power zuwa ga ministan,
Wannan babbar dama ce domin za ka iya samun aikin shirin N~ power cikin sauki ta wannan hanyar, wannan shi ne website din minista da zaku shiga domin tura bayananku:

👇👇👇👇👇👇👇👇

jobs.khadimiyya.org

2. Forms, har ila yau, minista kuma attorney general, ya rarraba forms a duk fadin jihar Kebbi, a wani bincike da JARIDARTALAKA ta yi, ta gano cewa, Barrister Abubakar Chika Malami SAN, ya rarraba forms dinsa zuwa kananan hukumomi 21 dake fadin jihar Kebbi,

Wannan forms ana sa ran duk wanda ya cika kamar yadda aka tsara, in shaa Allahu zai samu taimako daga wurin minista domin samun aikin shirin N~Power cikin sauki,

A wani bincike da JARIDARTALAKA ta yi, a wata karamar hukumar mulki da ake kira da suna "Bagudo" mutane da dama sun cika wannan form da ya fito daga hannun minista, domin sun ce sun yadda da minista kuma suna tunanin zai taimaka musu kamar yadda ya saba taimakon talakawa, domin sun ce dama taimako aikinsa ne,

Abdullahi Galadima wanda shine ambassador kuma youths leader na darikar Khadimiyya reshen karamar hukumar mulki ta Bagudo da kuma Jafar Abubakar Malami, da Abdullahi Umar Kaliel na daya daga cikin mambobi na darikar "Khadimiyya" reshen karamar hukumar mulki ta Bagudo, sannan su ne wakilan minista da suka gudanar da aikin cika form din na minista,

Abdullahi Galadima Ambassador, ya tabbatar wa JARIDARTALAKA cewa, duk wanda ya samu nasarar cika wannan form, to ya dauka cewa tamkar an dauke shi aikin N~ power da yardar Allah, domin minista mutum ne mai son ganin talaka ya samu walwala a kodayaushe.

To sai dai a wata hira da muka yi da wata mai suna "Uwani Koko" a garin Koko ta hanyar salula, ta tabbatar muna da cewa, tana ganin kamar wannan form na minista bai iso a garin na Koko ba, domin ta ce gaskiya ba ta taba jin wani labari irin wannan a garin Koko ba, sai dai ta ce wannan abinda ta sani kenan, babu mamaki an kawo sai dai bata sani bane kawai.

Daga:
Mohammad Aminu Bagudo,
07045466415

No comments

Powered by Blogger.