Header Ads

Header ADS

Matsalata da masu neman aurena ~ Inji jaruma Shalele Umar


RAHAMA Umar jaruma ce kuma mawaƙiya wadda ta shigo Kannywood da ƙafar dama. Dalili shi ne mace ce kyakkyawa son kowa ƙin wanda bai samu ba, mai ladabi da biyayya ga na gaba da ita, kuma Allah ya ba ta hazaƙa. Ta iya aktin, ta iya waƙa. Wannan ya sa tun da ta shiga harkar fim tauraruwar ta ke ɗagawa.
 
To amma Rahama, wadda ake yi wa laƙabi da Shalele, ta na fuskantar irin matsalolin da wasu matan da su ka shiga harkar fim su ke fuskanta, musamman idan an zo neman auren su. Shin wace matsala ce wannan? Ku karanta wannan hirar tata da mujallar Fim ku ji.
 
 
FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin ki a taƙaice.
 
SHALELE UMAR: Da farko dai suna na Rahama Umar, amma an fi sani na da Shalele Umar. Na yi firamare na a Na’ibawa Special Primary School, Kano,  na yi sakandare na a Kano, sannan na yi Sa’adatu Rimi Collage of Education, inda na karanta Integrated Science, I.S.C.G.M. kenan, double measure kenan.
 
FIM: Ke wace yare ce?
 
SHALELE (ta yi dariya): Gaskiya ni girman Kano ce, amma asali mu ‘yan Lokoja ne, Jihar Kogi.
 
FIM: Yaren ki fa?
 
SHALELE: Egbira Koto. Ni ‘yar Koton Karfe ce.
 
FIM: Ya aka yi ki ka tsinci kan ki a Kannywood?
 
SHALELE: Gaskiya da farko na fara ne da zuwa irin su maulidi, idan mu ka je Lokoja haka ina zuwa maulidi mu na waƙoƙi irin na Islamiyya. Daga nan dai na fara  sha’awar harkar waƙa. A haka na fara faɗa wa Mama na cewa ni ina so in rinƙa yin waƙa irn na ƙasida, sai ta ce min a ina ake yi? Na ce mata a situdiyo ake yi. Sai ta ce ni na san situdiyo ne? Na ce mata, "Wallahi ban sani ba, amma na san wani a unguwar nan shi ma ya na harkar." 
 
Da na je na tambaye shi sai ya ce zai kai ni situdiyo, amma sai na zo da shi gida tukunna. Da na zo da shi gida aka gama magana, sai aka ce in rinƙa zuwa da ƙanwa ta. Mu ka fara zuwa, aka ba ni lokaci. Idan mun je ƙarfe tara, sai mu dawo ƙarfe sha biyu. Haka na ci gaba har zuwa lokacin da Allah ya yi na zama jaruma. Ka san in ka je wuri da wata manufar, sai Allah ya juya maka lamari, sai na dawo harkar fim.
 
FIM: A wancan lokacin kin yi waƙoƙi ne?
 
SHALELE: E, gaskiya na yi su, sai dai matsalar da aka samu. Kuma a lokacin ina iya rubutawa, ana kuma rubuta min. Haka cikin hukuncin Allah na yi bidiyon waƙoƙin da kai na, na kai su wurin tacewa a Zoo Road a wurin Murtala Turaki, sai dai kuma Allah bai nufa na fitar da su ba har yanzu! (ta yi dariya)
 
FIM: Kin yi waƙoƙi sun kai nawa?
 
SHALELE: Gaskiya su na da yawa. Na yi waƙoƙin siyasa, na yi na ƙasidu, na yi na soyayya. Amma na fi yin na siyasa yanzu.
 
FIM: Wace waƙa ce ki ka yi wadda za a iya gane cewa Shalele ce ta yi ta?
 
SHALELE: Na siyasa, na yi wa Sanata Dino Melaye, na yi wa wani Kaftin Zakari, na yi wa Modibbo. Gaskiya na yi su da ɗan dama. Na yi wa kamfanoni da sauran su.
 
FIM: Na soyayya kuma fa?
 
SHALELE: Na soyayya gaskiya sai dai na hau.
 
FIM: Ya aka yi ki ka koma harkar fim daga waƙa?
 
SHALELE: Gaskiya ba ni na so fim ba. Ka san idan Allah ya sa abu zai faru, babu makawa sai ya faru. Ina waƙa, sai wani ya ce ya na so na je na yi masa amshi a Zoo Road. Sai na ce masa to. Da mu ka je sai Allah ya sa mu ka tarar da za a tafi lokeshin wurin ɗaukar fim, a lokacin ana jiran wata yarinya ba ta zo ba. Sai darakta Yahaya Sa’eed ya ce ga wata ma ta zo a tafi a yi da ita, sai ya ce a tafi da ni. Sai na ce ba ni da ra’ayin yin fim, gaskiya ba za ni ba. Su ka yi su ka yi da ni in bi, su na ce a’a, tunda ban gaya wa iyaye na ba. Sai su ka ce gaskiya ne. A ranar dai ba su ma fita aikin ba. A nan sai ya karɓi numba na, ya ce zai zo ya yi wa iyaye na magana. Ya zo gidan mu da sassafe ya samu anti ya yi mata magana. Sai ta ce masa maigidan ba ya nan ya na ƙasar waje, amma idan ya dawo za a faɗa masa, ya yi haƙuri har ya dawo. 
 
A lokacin da ya dawo ya zo su ka yi magana. Ya tambaye ni ni ina so? Na ce masa ni ba ni da wani ra’ayi tunda dai ina harkar kuma duk ya na da kyau in an bar ni zan yi. Sai ya ce masa, "Amana na ba ka wannan yarinyar." 
 
Kuma shi ma (darakta) ya yi iya bakin ƙoƙarin sa, don ya fita da ni aiki ya na ƙoƙari wurin ganin ya keɓe ni daga  matan da su ka girme ni; idan ya ga ina yin wani abin da ba daidai ba, zai yi min magana da ido, sai in bari. A haka dai na fara har na zo na haɗu da wasu  mutanen a cikin harkar.
 
FIM: Kin yi finafinai za su kai nawa?
 
SHALELE: Gaskiya na yi finafinai, amma ba duka na riƙe sunan su ba. Har ma da irin wanda ake yin Turanci da Hausa, ‘River Between’.
 
FIM: Ki faɗa mana sunan wasu daga cikin su.
 
SHALELE: Ah to, gaskiya na manta.
 
FIM: Babu ko ɗaya da ki ka riƙe sunan shi?
 
SHALELE: Gaskiya ban riƙe ba. Duk sun ɓace min ne gaskiya.
 
FIM: Wane irin cigaba ki ka samu a cikin harkar fim?
 
SHALELE: Gaskiya alhamdu lillahi, tunda ka ga dai kowa da manufar da ya shiga da shi: idan ka shigo da manufa mai kyau, Allah zai taimaka maka, tunda ka ga ni farko iyaye na ne su ka sa ni, su ka yarda na fara. Ko lokacin da aka tantance ‘yan fim a Hukumar Tace Finafinai da ‘yan’uwa na na je gaba ɗayan mu; har da mahaifiya ta da ƙanan yara waɗanda ake shayarwa mu ka je. A lokacin cikin masu tantancewar har da Ruƙayya Dawayya, har ta ce ta ji daɗi da ta ga iyaye na da ‘yan gidan mu dukkan su sun zo, ta ce haka ake so idan mace za ta shiga fim iyayen ta su amince. Su ka yi magana da mama na sosai, ta ce mata, "Mama ki yi mata addu’a." Addu’ar nan kuma ta na bi na. Duk da cewa duk wanda ya shiga fim ya na so duniya ta san shi, gaskiya ni ba mai son yawan jama’a ba ce, shi ya sa na ke gefe-gefe. Ba kuma ban san yadda zan yi in ɗaukakan ba ne, a’a, na fi so ina gefe. Kuma a hakan ina samu, tunda ina waƙoƙi ina kai wa kuma ana yi min alheri.
 
Shalele Umar a lokacin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ta cikin watan Yuni 2020
 
 
FIM: A ɓangaren ƙalubale kuma fa?
 
SHALELE: Gaskiya akwai. Saboda duk da iyaye na sun yarda da in yi fim, amma wasu daga cikin ‘yan’uwa na su Na ganin ‘ya mace dai ya kamata ta yi aure, tunda na girma. Wasu kuma za su kira ni a waya su ce su na so na, wasu su ce ina burge su, wasu kuma za su ce su na son ka, amma harkar nan da ka ke yi ne matsalar. 
 
Babban ƙalubalen da na fi fuskanta shi ne idan na samu mijin aure  in an fara magana da gaske za a yi auren, in ya gane cewa ni ‘yar fim ce sai ya janye, ba wai kuma don ba ya so na ba ne, sai ya ce iyayen sa idan ya ce masu ‘yar fim ce ba za su amince ba. Wannan }alubalen shi na ke samu a yanzu.
 
FIM: Wanene ubangidan ki?
 
SHALELE (ta yi dariya): Shu’aibu Lilisco ne ubangida na. Amma fa su biyu ne, don ba zan manta da wanda ya kawo ni ba, wato Yahaya Sa’eed; shi ne asalin ubangida na.
 
FIM: Wane jarumi ki ka fi son a haɗa ki da shi a fim?
 
SHALELE (dariya): Gaskiya ina son Sadiq Sani Sadiq, da dukkan jaruman irin su Ali Nuhu. Duk wanda aka haɗa ni fim da shi ina so.
 
FIM: A ɓangaren mata fa?
 
SHALELE: Babu wadda ba na so, irin su Rahama Sadau takwara ta; Hadiza Gabon, mahaifiya ta na son ta, saboda haka na ke son ta ita ma.
 
FIM: Wane kamfani ne ki ka fi sha’awar kasancewa a ƙarƙashin shi?
 
SHALELE: Ka san abin na Allah ne, amma kowa na son abu mai kyau.
 
FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa masoyan ki?
 
SHALELE: Ina yi masu godiya da irin yabo na da su ke yi idan su ka ga aiki na, musamman irin na barkwanci da na ke yi na ke sakawa a soshiyal midiya. In-sha Allahu zan ci gaba da faranta masu rai.


Tura wannan labari zuwa WhatsApp:

No comments

Powered by Blogger.