Header Ads

Header ADS

Labarin matar da ke auren maza biyu (2) a lokaci guda kuma suke zaune a gida guda ~ Karanta labarin a nan


Aure dai lamari ne mai muhimmanci a cikin al'umma na duniya daban daban inda mutane biyu da ke kaunar juna kan amince su zauna tare don soyayya da taimakon juna. A Najeriya da mafi yawancin kasashe na Musulunci na miji ne ke auren mace kuma galibi yana iya auren mace fiye da daya idan yana da hali. 

Sai dai a yanzu zamani ya canja har ta kai ga wasu matan suna auren mazaje biyu ko fiye kuma su zauna da su lafiya a gida ɗaya su haifa musu yara. Wata mata mai amfani da dandalin sada zumunta ta wallafa hotunan ta tare da maza biyu da yara da ta ce mazanta ne kuma suna zaune lafiya. 

Kenya Stevens mace mai maza biyu ta ce har yanzu tana iya tsunduma wa cikin kogin soyayya da wani idan tasu ta zo ɗaya. Hotunan wata mata da ta auri maza biyu kuma suke zaune gida daya.

Ta wallafa hotun mazanta biyu, Rakhem Seku, mai bawa mutane shawarwari kan zamantakewar soyayya kuma marubucin littafai. Tana kiran su 'Hubby 1' da 'Hubby 2' wato miji na farko da miji na biyu har wasu lokutan ta ke yi musu ba'ar cewa za ta ƙara miji na uku.

Ta ce sun kwashe shekaru tare da mazan biyu kuma ta haifa musu yara har ma sun girma. Su kan wallafa hotunansu tare a dandalin sada zumunta ta Instagram inda za a gano su cikin annashuwa.

Kenya ta ce mazajen nata biyu suna zaman lafiya, su kan yi yawancin harkokin su na yau da kullum kamar gyaran mota da wasu abubuwan tare. Ta kuma ce ba gaskiya bane ikirarin da ake yi cewa maza sun fi mata sha'awa sai dai kawai an daɗe ana dakushe mata ne shi yasa suke danne sha'awarsu. 

No comments

Powered by Blogger.