Header Ads

Header ADS

Jaruman fina-finan Hausa za su more wani abin alheri daga gwamnatin Kano: Ganduje


WANI kamfani mai zaman kan sa ya gabatar wa da gwamnatin Jihar Kano wani tsari kan yadda za ta gyara masana'antar finafinai ta Kannywood domin a samu ƙarin kuɗin shiga.
 
A takardar sanarwa ga manema labarai da mai ba gwamna shawara kan aikin jarida, Abba Anwar, ya rattaba wa hannu, wadda mujallar Fim ta samu, an bayyana cewa kamfanin, mai suna 'Credent Capital and Advisory', ya gabatar da shawarwarin sa ne a cikin wata takarda da shugaban kamfanin ya miƙa wa gwamnatin a ranar Laraba, 26 ga Agusta, 2020.
 
A yayin da ya ke gabatar da jawabin sa a gaban majalisar zartaswa ta jihar a Gidan Gwamnati (Africa House), Kano, Manajan Darakta na kamfanin, Dakta Charles A. Kachill, ya nuna damuwar sa kan abin da ya kira rashin samun kuɗin shiga ga Kannywood sakamakon rashin kyakkyawan tsari saboda rashin kataɓus ɗin 'yan masana'antar da sauran masu ruwa da tsaki.
 
Mista Kachill ya bayyana cewa kamfanin sa zai haɗa hannu da gwamnatin Jihar Kano don a yi wa masana'antar garambawul.
 
 Ya ce, "Kannywood fa industiri ce wacce darajar ta ta haura dala miliyan ɗari takwas ($800m). To amma ba a tsara ta yadda za ta ci moriyar shirye-shiryen da ke akwai a ƙasa ba daga Gwamnatin Tarayya da sauran hukumomi da ƙungiyoyin ƙasashen waje.
 
"Saboda haka ya kamata a gyara ta yadda za ta zama masana'anta ta gaske sosai."
 
Bugu da ƙari, ya ce, "Mu na magana ne kan matasa sama da miliyan biyu da za su iya samun aikin yi a masana'antar. Mu na da furodusoshi, daraktoci, 'yan wasa maza da mata, marubuta, 'yan kasuwa, masu raba finafinai, masu kyamara, mamallaka gidajen sinima, da sauran su da dama."
 
Shugaban kamfanin ya faɗa wa majalisar cewa kamfanin sa na Credent ya na so ya zama babban mai ɗora masana'antar a kan turbar cigaba a yayin da ita kuma gwamnati za ta mara masa baya wajen tabbatar da an yi duk abin da ya dace.
 
Haka kuma ya bayyana cewa akwai buƙatar a gyara wannan masana'anta ta nishaɗantarwa ta yadda za a ci moriyar ta sosai a jihar, musamman wajen samun kuɗaɗen shiga ga gwamnati. 
 
Mista Kachill ya kawo shawarar a kafa wani kamfani na kasuwanci wanda gwamnatin jihar za ta riƙa gudanarwa, wanda ta hanyar sa za a riƙa isar da tsare-tsare ga 'yan fim ɗin da ke masana'antar Kannywood kamar yadda ya kamata.
 
Bayan ya gama jawabin sa, sai Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi nasa jawabin, inda ya ce majalisar zartaswar za ta duba takardar da Mista Kachill ya kawo domin ta yanke shawara a kai.
 
A takardar sanarwa ga manema labarai da mai ba gwamna shawara kan aikin jarida, Abba Anwar, ya rattaba wa hannu, an ce gudanar da wasu ayyuka ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa ya na daga cikin muhimman tsare-tsaren wannan gwamnatin ta Jihar Kano.

No comments

Powered by Blogger.