Header Ads

Header ADS

Hukumar 'yan sanda a Najeriya ta samu wata babbar kyauta ~ Jaridartalaka
An bawa hukumar 'yan sandan Najeriya motoci masu kyau - Hukumar 'yan sandan ta samu kyautar motocin ne guda uku daga wurin kamfanin motoci na Najeriya na Innoson domin taimakawa wajen gabatar da ayyuka a fadin kasa A kokarin da take na taimakawa al'umma, kamfanin motoci na Innoson dake Najeriya ya bayar da kyautar motoci guda uku ga hukumar 'yan sandan Najeriya. 

A sanarwar da kakakin hukumar 'yan sandan na kasa, Frank Mba, ya fitar, shugaban hukumar 'yan sanda na kasa ya karbi wadannan motoci guda uku daga wajen wannan kamfanin. Motocin masu kirar Innoson G12 Series, an mika su ga hukumar 'yan sandan Najeriyan ta hannun Jonas Maduabuchukwu Ojukwu a madadin shugaban kamfanin Cif Innocent I. Chukwuma. 

Shugaban hukumar 'yan sandan da ya samu wakilcin DIG Abdulmajid Ali, ya bayyana cewa "bayar da taimako a wannan yanayi, babu shakka hukumar 'yan sandan Najeriya za ta samu nasarar kawo karshen ta'addanci a kasar nan." Ali ya bukaci sauran al'umma da kamfanoni da suyi koyi da wannan halayya mai kyau. 

Latsa nan domin biyo mu a shafin Twitter

Tura wannan labari:

No comments

Powered by Blogger.