Header Ads

Header ADS

Coronavirus ta kashe wani chairman a Najeriya har lahira


Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Onigbongbo a Legas, Mr Babatunde Oke rasuwa.
Ya rasu ne a safiyar yau Laraba 12 ga watan Agusta sakamakon cutar COVID-19 wacce aka fi sani da korona.
A cewar sakon da aka wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta ta Facebook, Oke ya rasu a yau a asibitin St. Nicholas da ke Legas Island inda aka mayar da shi lokacin da ciwon ya yi tsanani.


Da farko ana kula da shi ne a cibiyar killace masu korona da ke Gbagada.
Oke yana kan waadin mulkinsa na biyu a matsayin shugaban karamar hukuma.
Shine shugaban karamar hukuma na biyu da annobar korona ta yi ajalinsa a jihar Legas.
A watan Yuni, shugaban karamar hukumar Agbado/Oke-Odo LCDA, Augustine Adeoye Arogundade shima ya mutu sakamakon kamuwa da cutar da COVID-19.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:


No comments

Powered by Blogger.