Header Ads

Header ADS

An yanke wa wasu mutane hukuncin shekaru 30 a gidan yari saboda jifar shugaban kasa da suka yi


Wata kotu a Burundi ta ɗaure wasu shekaru 30 da suka ƙunshi maza biyu da mace ɗaya saboda sun jefi ayarin shugaban kasa.


Kotun ta kama su da laifin yunƙurin halaka shugaba Evariste Ndayishimiye.
An zarge su da jifan ayarin shugaban da duwatsu lokacin da ya ziyarci lardin Kayanza da ke arewacin kasar a Larabar da ta gabata.


Mai gabatar da ƙara ya nemi a yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru bakwai saboda jifa da duwatsu, yayin da kuma kotu ta ce ta kama su da laifin yunkurin halaka shugaban tare da yanke masu hukuncin ɗaurin shekaru 30.
A wannan watan ya kamata a rantsar da shugaba Evariste Ndayishimiye bayan ya lashe zaben da aka gudanar watan Mayuamma aka rantsar shi a watan Yuni saboda mutuwar shugaba Pierre Nkurunziza da ya gada.

No comments

Powered by Blogger.