An kashe dan majalisa tare da sace matansa biyu a Najeriya ~ Jaridar Talaka
Rahotanni daga Jihar Bauchi sun tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar ta tabbatar da kisan dan Majalisar da ke wakiltar mazabar Dass, Hon Musa Mante Baraza a daren jiya Alhamis.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi, DSP Ahmad Muhammad Wakil ne ya tabbatar da labarin a safiyar yau Juma’a. Inda ya kara da cewa ‘Yan bindigan bayan sun kashe dan majalisar, sun kuma sace matansa biyu da diyarsa.
Kakakin ya ce: “Matansa biyu da aka Sace su ne; Rashida Musa Mante, Rahina Musa Mante da yarsa ‘yar shekara daya, Fausar Musa Mante.”
Tura wannan labarin zuwa:
Facebook
WhatsApp da
Twitter.
No comments