Header Ads

Header ADS

An kama matasan da suka yi askin rashin da'a a NajeriyaJihar Kano na daya daga cikin jihohin Najeriya dake kokari wajen ganin cewa ta daidaita al'amuran yau da kullum a duk fadin jihar,

Dakarun hisbah ne da kansu suka damko wasu matasa da suka yi askin rashin da'a ranar bikin babbar sallah,

Dakarun na Hisbah sun damko duk wani matashi da ya yi banzan aski a ranar bukukuwan babbar sallah karkashin jagorancin kwamandan hisbah na jihar Kano, Dr Ustaz Harun Mohammad Sani Ibn Sina.

Matasan wadanda suka yi banzan askin da ya saba ma addinin musulunci wanda kuma ya saba ma al'adar malam Bahaushe, sun hadu da fushin hukumar hisbah ta jihar Kano a wurare daban daban,

Dakarun Hisbah sun sha alwashin cewa. Za su kakkabe duk wasu dabi'u na rashin da'a da suka saba ma addinin musulunci da wasu matasa ke aikata wa,

A ya yin da yake shawartar matasan, babban kwamandan hisbah Ustaz Harun Mohammad Ibn Sina, ya yi kira zuwa ga matasan da su kasance masu aikata ayyuka na gari domin al'ummar duniya su yi alfahari da su.

No comments

Powered by Blogger.