Allah ya yi ma sarkin Tambuwal rasuwa ~ Karanta cikakken labarin a nan
Al’ummar Jihar Sakkwato sun wayi gari
da alhini da jimamin rasuwar Mai Girma Sarkin Tambuwal, Alhaji Mainasara Attahiru.
A sanarwar rasuwar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya sanyawa hannu da sanyin safiyar yau ya bayyana cewar Basaraken ya rasu a jiya Alhamis bayan fama da gajeriyar rashin lafiya a Abuja, kuma za a yi jana’izarsa a yau Juma’a a Tambuwal.
“Cike da fauwalawa Allah lamurransa, a madadin Gwamnati da al’ummar Jihar Sakkwato nake sanar da rasuwar Mai Girma Sarkin Tambuwal Alhaji Mainasara Attahiru. Ya bayyana.
Haka ma Gwamnan ya roki Allah madaukakin Sarki ya gafartawa mamacin ya karbi bakuncinsa ya kuma sa Aljanna Firdaus ta kasance makomarsa.
Dan girman Allah Da Annabi Tura Wannan Labarin Zuwa:
1. Facebook
2. WhatsApp. Ko kuma
3. Twitter
No comments