Header Ads

Header ADS

Abin takaici: An kama wasu mutum 3 masu kawo wa 'yan bindiga makamai a jihar Sokoto


Wasu yan kasar Nijar uku sun shiga hannu a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto sakamakon safarar makami da fasa kwabri.

 Jagoran yada labaran hukumar tsaro, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan ranar Juma'a a hira da manema labarai. Enenche ya ce mutanen uku mambobin wata kungiyar masu safara makamai ne a yankin.

 Ya bayyana cewa suna shigo da makamai Najeriya ta hanyar boyesu cikin motocinsu. "Dakarun Operation SahelSanity da aka tura karamar hukumar Sabon Birni ranar 15 ga Augusta sun samu nasarar wargaza wani gungun masu safarar makamai da suka kware wajen kaiwa yan bindigan Arewa maso yammacin Najeriya makamai daga kasashen ketare."

 "Dukkan mutane ukun yan kasar Nijar ne kuma an kamasu ne a Dantudu dake karamar hukumar Sabon Birni da bindigar AK-47 guda shida, carbin AK-47 hudu da harsasai 2,415 boye cikin motocinsu.

" Enenche ya laburta. Kakakin hukumar tsaron ya kara da cewa matsalar rashin tsarona wasu sassan Najeriya na da sa hannun kasashen waje. Enenche ya tuna cewa an damke wasu turawa biyu masu safarar makamai a jihar Nijar. An damke yan kasar Nijar 3 masu safarar makamai a jihar Sokoto.

Tura wannan labari zuwa:
WhatsApp
Twitter da 
Facebook.

No comments

Powered by Blogger.