Header Ads

Header ADS

Zan kawo sauyi a masana'antar shirya fina-finan Hausa da manyan mata - Abdul Amart Maikwashewa


Babban furodusa kuma fasihi a fagen shirin fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood wato Abdul Amart Maikwashewa, ya ce zai kawo wani sabon salo na daban a cikin fim dinsa da zai fara aiki a kwanan nan mai suna 'MANYAN MATA'

Maikwashewa ya ce zai fi maida hankalinsa wajen inganta fim maimakon neman kudi da shirin fim din soyayya, domin inganci shi ne abinda tarihinsa ba zai taba dusashewa ba,

Abdul Amart ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake tattaunawa da Mujallar Fim a wurin wani taro na karrama wadanda suka yi nasara akan gasar fim dinsa da ya saka a jihar Kaduna,


Abdul Amart shi ne shugaban mashahurin kamfanin nan mai shirya fina-finan Hausa wato 'Abnur Entertainment', kuma ya yi bayanin saka gasar wannan sabon fim dinsa tun a ranar Litinin, 15 ga watan Yunin shekarar 2020 a garin Kaduna,

Babban Furodusan ya shirya wannan gasar a shafinsa na Instagram dake da dubban mabiya, kuma ya tsara tambayoyi masu wahalar amsawa inda ma ake ganin kamar sai wadanda suke da kusanci dashi ne kadai za su iya amsa tambayoyin,

Tun a ranar 5 ga watan Yuli, Abdul Amart ya bayyana wadanda suka lashe gasar tun daga mutum na 1 har zuwa na 20, tare kuma da bayyana ranar da za a raba kyaututtukan ga wadanda suka yi nasarar lashe gasar,

Daga karshe dai an yi bikin karramawar a gidan cin abincin Rahama Sadau wato 'Sadauz Home' dake lamba 27 titin rabah dake jihar Kaduna.

Latsa link din dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.