Header Ads

Header ADS

Za a baiwa matasan Najeriya tallafin kudade domin inganta sana'o'insu - Gwamnatin Tarayya


A kokarinta na magance talauci a tsakanin matasan da ke da karamin karfi, gwamnatin tarayya ta amince wajen fitar da zunzurutun kudade har kimanin naira biliyan 75 domin tallafa wa matasa akan sana'o'insu,

A cewarsa, ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko a cikin tarihin Najeriya da matasa suka samu wani abun cigaba wanda za a iya kira 'Bankin Matasa' kai tsaye,

Ministan ya kara da cewa, wannan tallafin zai fara ne daga masu shekaru 18 zuwa 35, su ne wadanda zasu ci gajiyar wannan shirin, kuma za a cika wannan neman tallafin ne ta hanyar yanar gizo, inda zaka rubuta dukkan abubuwan da ake bukata, kuma za ka samu tallafin idan har ka cancanta,

Dare ya kara bayyana cewa, majalisar zartarwar Najeriya ce ta amince da wannan kudurin, kuma za a baiwa dukkan wanda ya cancanta ba tare da nuna bambanci ko kabilanci ba.

Kamar dai yadda gwamnatin Najeriya ke ikrarin cewa za ta baiwa matasa tallafin kudade domin inganta sana'o'insu tare da samar da guraben ayyuka ga wadanda suka yi karatu,

Za a iya cewa wannan babbar dama ce ga dukkan matashi da ya hanzarta kada ya yi kasa a guiwa wajen cika wannan tallafin da zarar an fara.

Latsa link dinnan dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇


https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.