Header Ads

Header ADS

To fa! Tsohon mawakin Hausa Mahmud Nagudu ya yi wata magana akan Annabi Muhammad PBUH


Duk wani Bahaushe mai sauraron mawakan Hausa na zamani zai yi wuya ya ce bai san wani mawaki mai suna Mahmud Nagudu ba,
Tsohon mawaki ne a masana'antar shirya fina-finan Hausa dake da cibiya a Kano,

Mahmud Nagudu ya yi kira da babbar murya zuwa ga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano da cewa, kada hukumar ta kuskura ta sa mawakan yabon Annabi Muhammad S.A.W a cikin kwamitin da za ta kafa da ya shafi wannan bangaren,

Mahmud Nagudu wanda idan ana maganar da ta shafi wakokin yabon manzo to tabbas shi ma kwararre ne kwarai da gaske, kuma ya yi wannan kira ne a lokacin da yake tattaunawa da Mujallar Fim.

Yana kira ga hukumar tace fina-finan da ta yi amfani da wadansu mutane na daban wajen tace wakokin fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W, kada a yi amfani da mawaki ko daya a cikin wannan kwamitin da za a kafa,

Yana tunanin cewa, wata kila idan aka yi amfani da mawaki hakan zai iya kawo rudani, a maimakon tantance wani can daban sai ka iske kila mawakin ne da kansa ke bukatar a tantance sa da kansa,

Kuma idan za a kafa kwamitin na tantance wakokin yabo, ya kamata a yi amfani da mutanen da waka ba sana'arsu bace, amma suna da ilmin addini da fahimtar juna, domin duk wani musulmi yana da alaka da manzon Allah A duk inda yake a fadin duniya.

Idan baku manta ba cikin kwanakin nan ne hukumar tace fina-finan Hausa da wakoki ta bayyana cewa za ta kafa kwamitin da zai rika tace wakokin da suka shafi addinin musulunci,

Wannan lamarin dai ya janyo musayar ra'ayoyi masu zafin gaske, inda wasu ke ganin dacewar hakan wadansu kuma akasin hakan,

Sai dai wani fitaccen mawakin yabon Annabi Muhammad S.A.W, Malam Bashir Dandago ya yi kira ga hukumar tace fina-finan Kano da su tabbatar sun yi amfani da mawakan yabon Annabi a cikin kwamitin da za ta kafa.

A wata hira da ya yi da mujallar fim, Malam Bashir Dandago ya bayyana cewa idan malaman addini kadai aka saka, tabbas ba zasu yi wa mawakan adalci ba, domin kuwa akwai wata dadaddiyar jayayya a tsakaninsu.


To amma a bangaren Mahmud Nagudu yana ganin cewa malamai kadai ya kamata su yi aiki a wannan bangaren, ya ce a nemo malamai masu ilmin addini, balaga, wadanda kuma suka san yadda ake shigar da magana,

Nagudu ya kara da cewa, wata magana idan aka fada wa mutum tamkar yabo ce, amma da zarar an fadawa Annabi ita, tamkar aibata shi ne, ya bayyana dokar a matsayin ingantacciya, domin tun da aka samar da duniya babu wani abu da ya kai darajar Annabi Muhammad S.A.W, saboda haka abu ne mai kyau a tsafta ce wakokin yabon manzon Allah.

Ya kara da cewa idan za a nemo malamai to a samu masu tsoron Allah, wadanda suke kaunar Annabi Muhammad S.A.W tsakaninsu da Allah, kada a kira dan Sunna, ko dan Tijjaniya, ko kuma dan Kadiriyya masu rashin fahimtar juna,

Wata kila idan dan Tijjaniyya ya yi hukunci sai dan sunna ko dan Kadiriyya su ga kamar ba a musu adalci ba, saboda haka duk wa danda za a kawo a tabbatar malamai ne masu ilmi, masu fahimta, sannan masu kaunar Annabi Muhammad S.A.W tsakaninsu da Allah.

Latsa link dinnan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.