Header Ads

Header ADS

To fa! Obasanjo ya ce yana son shiga aljanna ~ Karanta dalili a nan


Tsohon shugaban kasar tarayyar Najeriya Olusegun Aremu Obasanjo ya bayyana cewa yana matukar son shiga aljanna domin yana son haduwa da mawakan aljanna,

Shugaban ya yi wannan furucin ne a lokacin da ya ji wata waka da mawakan Apostolic Faith Church dake garin Igbesan jihar Ogun suka rere,

Har ila yau, tsohon shugaban ya yiwa kiristoci wa'azi da su ji tsoron Allah, Sannan su kasance cikin shiri domin Isah Al-masihu zai zo a karshen duniya,

Obasanjo ya kara da janyo hankalin mabiya addinin kirista cewa, "ya kamata su shirya sosai, domin Ubangiji yana nan dawo wa, kuma akwai wani abokinsa da ya fada masa cewa, idan suka mutu suka shiga aljanna, sai mun gaji da rera wa Ubangiji waka"

Kuma aljanna za ta zama kamar kurkuku (Gidan Yari) Babu dadin zama, in ji tsohon shugaban kasa Obasanjo.

To sai dai Obasanjon ya ce, shi kamar yadda yake gani, tabbas zai shiga aljanna, sannan kuma zai kasance a cikin kungiyar mawakan aljanna, ya kara da cewa, idan har wannan waka da yake ji irin misalin wakokin mawakan aljanna ne da suke rera wa Ubangiji, tabbas ya ce yana son shiga cikin wannan kungiyar mawakan aljanna.

Shugaban ya kara da cewa, Isah Al-masihu ya zo duniya ne domin ya nuna musu yadda rayuwa take sannan kuma ya ceto su daga fadawa hanyar halaka, wannan shi ne dalilin zuwan Al-masihu a wannan duniya,

"Allah Zai iya gyara Najeriya, amma dole sai mun kira shi domin ya shigo cikin rayuwarmu kafin mu samu taimako daga gare shi, sannan duk wani abu da zamu yi a kasar nan ai hannunmu yake" In ji tsohon shugaban kasa Olusegun Aremu Obasanjo.

Latsa rubutun dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:🇳🇬👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.