Header Ads

Header ADS

To fa! Kwankwasiyya ta maka Ganduje a kotu - karanta dalili a nan


Kungiyar Kwankwasiyya mai babban reshe a jihar Kano kuma wadda ke karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Dr Rabi'u Musa Kwankwaso ta maka gwamna mai ciki Dr Abdullahi Umar Ganduje a Kotu domin hana shi ciyo bashi daga kasar China,

Babbar kungiyar Kwankwasiyya reshen jihar Kano sun maka gwamna Ganduje Kotu ne domin hana shi ciyo bashi daga kasar China wanda ya kai kimanin €684,100.100.00 daga China Development Bank, domin samar da kudaden da za a yi aikin jiragen kasa a duk fadin jihar,

Kungiyar Kwankwasiyya ta rubuta korafi akan gwamnatin Kano, da kuma majalisar dokokin jihar Kano zuwa ga shugaban majalisar dattawa a Najeriya, ma'aikatar kudi ta kasa, ofishin ba da bashi na kasa, ofishin jakadanci tsakanin China da Najeriya, da kuma China Development Bank,

Kwankwasiyya ta rubuta cewa an saba ka'ida cikin yarjejeniyar ciyo wannan bashin, kamar yadda jaridar nan ta intanet 'DAILY NIGERIAN' ta ruwaito,

A cikin wata sanarwa da dan takarar mataimakin gwamna a jam'iyar PDP a shekar 2019 wato Aminu Abdulsalam ya sanya wa hannu ya bukaci kowa da kowa ya kalubalanci wannan bashi da Ganduje yake shirin ciyo wa,

Aminu Abdulsalam yana zargin cewa, idan har aka amince wa gwamna Ganduje ya ciyo wannan bashin, tabbas babu wani aiki da Gandujen zai iya yi, illa dai kudin zai ajiye su ne a aljihunsa.

Source: alummata.com

Latsa rubutun dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.