Header Ads

Header ADS

Tirkashi: Yadda aka kama masu damfarar mutane da sunan masarautar Katsina


Asirin wasu mutane masu damfarar manyan mutane da sunan sarkin Katsina ya cika bayan 'yan sanda sun samu nasarar kama su a cikin jahar.

Mutanen na amfani ne da sunan majalisar masarautar Katsina inda suke tura sakonnin waya zuwa ga manyan mutane suna neman taimako da a tura kudade zuwa wani asusun banki da sunan tallafi ga masarautar,

Kakakin 'yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya ce mutanen da suka riga suka cuci wasu manyan mutane na amfani ne a matsayin sakataren masarautar Katsina, Alh mamman ifo,

Masu damfarar sun yi amfani ne da cewa masarautar na neman tallafi ne domin aurar da wasu mata marayu, Gambo Isah ya ce kafin asirin 'yan damfarar ya tonu wanda ya hada da dan asalin jihar Katsina, da dan jihar Nasarawa, sun tura irin wadannan sakonni da dama zuwa ga manyan mutane da suka hada da:

Farfesa Ango Abdullahi, da Janar Muhammadu Buba Marwa, da Hon. Chairman Abdullahi Adamu Candido da kuma Umaru Ajiya - NNPC, da Manjo M.K Yusuf-Legas, da Sanata Sa'idu Alkali, da darekta Janar na hukumar NYSC - Birgediya Janar Shu'aibu Ibrahim da ma sauran wadansu manya-manyan mutane.

Daga:
Mohammad Aminu BagudoNo comments

Powered by Blogger.