Header Ads

Header ADS

Tabdijam: Wani matashi ya ce zai tayarda bam a dakin taron majalisar tarayya da kuma kamfanin NNPC idan har gwamnati bata bashi kayan tallafi ba!


Wata kotu a Najeriya ta yanke wa wani saurayi hukuncin shekara biyu (2) a gidan yari sakamakon laifin da aka kama shi da shi na yunkurin saka bam a dakin majalisar tarayya da kuma kamfanin man fetur na kasa NNPC, wai idan har aka kuskura aka ki bashi kayan tallafin COVID-19,

Wannan hukuncin an yanke shi ne a wata kotun majistire dake Lokoja babban birnin jihar Kogi dake Najeriya, to sai dai kuma ta ba da damar belin wannan matashin,

Wannan matashi ne dan shekaru 35 mai suna Adeoye wanda dan asalin karamar hukumar Okehi ne, bai musanta laifin da ake zarginsa da shi ba, domin ya amsa laifin sa lokacin da ake masa tambayoyi,

O. A Yahaya shi ne jami'in tsaro na DSS da ya gurfanadda saurayin a gaban mai shari'a A. S Ibrahim, kuma jami'in ya sake maimaita abinda saurayin ya yi ikrarin aikatawa in har ba a bashi kayan tallafin na COVID-19 ba.

Matashin wanda yanzu haka dalibi ne kuma shi ne kadai a wurin mahaifinsa, ya roki kotu da ta yi masa sassauci kuma ya yi alkawari ba zai sake yin wani abu kamar wannan ba,

Wannan shi ne dalilin da ya sa mai shari'a ya yi sassauci ga hukuncin zuwa shekara biyu (2) a gidan yari.

Shiga link din dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.