Header Ads

Header ADS

Shugaba Buhari ya aika sakon ta'aziyar sojar nan mace ta farko da ta fara tuka jirgin yaki


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya aika sakon ta'aziya cikin tausayi zuwa ga iyalan sojar nan da ta fara tuka jirgin yaki wato Mrs Tolulope Arotile, sojar sama ce wadda ta mutu a Kaduna,

Shugaba Buhari ya ce ya ji rasuwar har cikin jikinsa domin tana da kwazo wajen ganin cewa an kakkabe 'yan ta'adda inda ya kira ta da suna kwararriya kuma wadda ta iya sarrafa jirgin yaki domin ya gani da idonsa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kara da cewa yana mika sakon ta'aziya zuwa ga sojojin sama, jihar Kogi da kuma iyalanta baki daya, ya kara da cewa, tarihinta ba zai taba zama abin mantuwa ba, domin tana da juriya da nuna kwazo a wurin aiki.

Daga,
Mohammad Aminu Bagudo

No comments

Powered by Blogger.