Header Ads

Header ADS

Sheikh Mohammad Nuru Khalid ya faranta wa jaruman kannywood zuciya


Wannan magana babu batun yi mata istigfari, domin na san mai karatu yana da masaniyar cewa ana yawan samun sabanin fahimta tsakanin malaman addini da kuma masu shirya fina-finan Hausa, mafi yawan al'umma suna goyon malamai ne domin suna zargin cewa, 'yan film din babu wani abu da suke kokarin yi in banda lalata tarbiyar kananan yara da ma sauran al'umma, inda su kuma 'yan film din suke ikrarin fadakarwa suke zuwa ga al'umma,

Daga cikin jaruman babu wani daya da malaman suka ware wanda suke kallon sa a matsayin mutumen kirki, domin matsalar ta shafi dukkan jarumai ne, to sai dai duk da haka, akwai wadansu jarumai fitattu da suka fi shan suka daga malaman addini, ciki akwai Adam A. Zango, Ali Nuhu, Ado Gwanja, Nura M. Inuwa, Umar M. Shareef da sauransu,

Idan aka zo ta fannin mata akwai irinsu, Rahama Sadau, Hadiza Gabon, Jamila Nagudu, Aisha Tsamiya, Fati Washa, Tima Makamashi da dai sauransu.

To sai dai a wata lakca da wani fitaccen malamin addinin musulunci ya gabatar, Sheikh Mohammad Nuru Khalid, ta sanya jaruman janye zargin da suke wa dukkan malaman addini, inda suka ce ashe dai akwai malaman da suke fahimtar manufofinsu, cikin jaruman akwai irin su Malam Aminu Saira, Ali Gumzak, Ali Nuhu, Saifullahi Safzor da dai sauransu.

Dukkan jaruman sun yi ta raba bidiyon lakcar da Sheikh Mohammad Nuru Khalid ya yi a shafukansu na sada zumunta irinsu Twitter da kuma shafin Instagram.

Shiga nan domin karanta sauran labaranmu
                         👇
www.jaridartalaka.com.ng

No comments

Powered by Blogger.