Header Ads

Header ADS

Mamaki: Shugaba Buhari ya ce a cikin gida zai yi sallar idi, kuma baya son kowa yazo mishi gaisuwar sallah


A wani mataki na inganta lafiya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a cikin gida zai yi sallar idi tare da iyalansa, wato Villa kenan fadar gwamnatin tarayyar Najeriya,

Malam Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasa ne ya sanar da hakan a babban birnin tarayya Abuja,

Malam Garba Shehu ya ce, idan ba a manta ba, ko a lokacin bikin karamar sallah, shugaba Buhari a gida ya yi sallah tare da iyalansa, yanzu ma haka abin yake bisa shawara da amincewar majalisar addinin musulunci ta kasa,

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana taya dukkan al'ummar Najeriya murnar zagayowar bikin babbar sallah, sannan yana ba da shawara ka da mutane su kasance suna tururuwa a wuri daya, sakamakon wannan cutar COVID-19 da ake fama da ita a duk fadin kasar,

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, baya bukatar kowa ya zo mishi gaisuwar babbar sallah kamar yadda aka saba yi, kuma ya yi hakan ne domin kare kai daga yaduwa ko kamuwa da cutar CoronaVirus.

Latsa rubutun dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.