Header Ads

Header ADS

Lokacin da bawa yake shirin komawa ga mahaliccinsa


Kamar yadda wannan kalmar take cewa: Kullu nafsin za'iqatil maut, wato dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa, wannan magana babu shakka haka take, domin kuwa arzikinka ko talaucinka ba zai hana ka mutuwa ba,

Haka kazalika, yaranci ko tsufa wadannan ma ba zasu iya hana ka mutuwa ba, duk yanda kake ganin kana da koshin lafiya, wannan shi ma babu garantin cewa ba zaka iya mutuwa ba,

Wallahi idan cikin karkashin kasa zaka gina gida, wannan shi ma ba zai hana mutuwa ta riske ka ba idan lokaci ya yi, dole dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa.

Ita dai mutuwa kamar arziki take, domin idan lokaci ya yi babu makawa sai an yi shi, kuma tana zuwa ga dan adam bisa adalcin Allahu S.W.A, idan lokaci ya yi, akan yi wa muminai ishara tare da nuna musu ajalinsu ya zo kusa,

Wata rana Annabin Allah Annabi Yaqub ya yi addu'ar cewa, Allah kada ya dauki ransa har sai ya nuna masa ishara, Allah S.A.W cikin ikonsa ya ce an karba maka,

Ya Allah muna rokonka da ka ji tausayinmu ka tsarkake zukatanmu, ka hana mu aikata miyagun ayyukan da babu alkhairi a cikin su, ka bamu ikon yi maka biyayya, sannan ka ji tausayinmu ka saka mu daga cikin bayinka 'yantattu wadanda za su samu rahamarka.

Wannan sako ne daga Jaridar Talaka.

No comments

Powered by Blogger.