Header Ads

Header ADS

Gwamnatin Kano za ta yi wani aikin alkhairi zuwa ga al'ummarta


Abdullahi Umar Ganduje, zababben gwamna mai ci na jihar Kano, ya bayyana cewa gwamnati a shirye take domin fara aikin layin dogo mai amfani da wutar lantarki,

Sai dai wannan aikin shimfida layin dogo mai amfani da wutar lantarki da gwamnatin Kano ke shirin yi, ya zama wani abin kace - nace a tsakanin al'umma,

To sai dai kuma a yayin da wannan aikin ke daukar hankali, babbar darikar Kwankwasiyya kwatsam ta maka gwamnatin Kano a gaban Kotu, inda take neman a hana gwamnatin Kano karbo wannan bashi daga kasar China,

A martanin da gwamnatin ta mayar, ta ce duk wannan tsegumi ba zai saka ta ta janye kudirinta na ciyo bashi daga kasar China domin aikata irin wannan babban aiki na alkhairi,

Gwamnatin ta kara da cewa, duk wata suka da za a yi mata ba za ta damu ba, kuma sukar ba za ta hana ta yin aiki a jihar Kano ba, domin tana son yin aiki domin mayarda jihar Kano babban birni, wanda zai iya yin gogayya da manyan biranen sassan duniya,

Wannan aikin da gwamnatin Kano za ta yi, ba haka kawai bane domin sai da suka tuntubi masu ruwa da tsaki a wannan harkar, kuma gwamnatin ta samu tabbacin cewa, wannan aikin zai habaka tattalin arzikin jihar Kanon,

Bayan bunkasa kasuwanci da tattalin arziki, gwamnatin ta ce wannan aikin zai taimaka wajen yin jigilar amfanin gona da ma sauran kayayyaki wadanda al'umma za su ci moriyar su,

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2016 ne majalisar dokokin jihar ta amince da karbo wannan bashi har na tsawon dala 1,850,839,098 a matsayin jimillar kudin da aikin zai lakume,

Gwamnatin tarayya ta amince wa gwamnatin Kano wajen ciyo wannan bashin, domin ita ce ta yi ruwa da tsaki wajen karbo kudin daga wani babban banki a China mai suna "China Import - Export Bank,

Gwamnatin Kano ta kulla yarjejeniya da wani kamfani wanda zai mata wannan aikin mai suna " China Railway Construction Company" sannan kuma ta kafa kwamiti wanda zai jibinci al'amarin, karkashin jagorancin Alhaji Isyaku Umar Tofa,

Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya ce, ya yin kammala wannan aikin, ana sa ran cewa shimfidar layin dogon zai fara tun daga Janguza zuwa Bata, Jogana zuwa Bata, Dawanau zuwa Bata, da kuma daga Kwanar - Dawaki zuwa Bata.

Source: Daga jaridar "Rariya"

Latsa rubutun dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.