Header Ads

Header ADS

Fadar masarautar Katsina ta soke bukukuwan hawan babbar sallah - karanta dalili


Wata sanarwa kai tsaye da ta fito daga fadar mai martaba sarkin Katsina, Alh. Abdulmuminu Kabir Usman,ta bayyana cewa majalisar Katsina ta soke bukin hawan babbar sallah da ake yi duk shekara domin nuna murna da farin ciki akan zagayowar wannan rana,

Kamar yadda aka bayyana, majalisar ta soke wannan buki ne sakamakon rashin zaman lafiya na 'yan adda dake faruwa a wasu sassan jihar Katsina, da kuma cutar COVID-19 wadda har yanzu akwai sauran ta a cikin jihar ta Katsina,

Wannan sanarwa tana cikin wata takarda ce wadda Sakataren jihar Katsina ya sanya wa hannu wato Alh. Bello Mamman Ifo,

Ifo ya bayyana cewa, mai martaba ya umarce shi da ya sanya wa takardar hannu sakamakon 'yan bindiga dake kashe rayukan al'umma tare da lalata dukiyoyinsu da kuma iftila'in wannan cutar Coronavirus da har yanzu akwai sauran ta a cikin jihar Katsina,

A sakamakon haka, mai martaba ya umarci dukkan al'ummar masarautar Katsina da su zauna gida tare da yin adduar samun zaman lafiya cikin jihar Katsina da ma Najeriya baki daya.

Al'ummar jihar Katsina na cikin wani irin hali na rayuwa ba tabbas sakamakon hare haren da 'yan bindiga ke kaiwa babu zato babu tsammani, Wanda sanadiyar hakan mutane da dama sun rasa rayuka wadansu kuma dukiyoyi a wannan jihar,

Gwamnatin jihar tare da hadin guiwa da gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinsu wajen ganin cewa sun tabbatar da zaman lafiya tare da kare dukiyoyin al'umma a fadin jihar Katsina,

Muna rokon Allah ya kawo karshen wannan iftila'i da mutanen jihar Katsina ke ciki, tare da tabbatar da zaman lafiya a kasarmu Najeriya da ma duniya baki daya, Allahumma Amin.

No comments

Powered by Blogger.