Header Ads

Header ADS

Duba ka gani idan ka cancanta domin samun kudin tallafi daga gwamnatin tarayya


Idan baku manta ba, kwanakin baya 'jaridartalaka.com.ng ta kawo muku bayanin ba da kudin tallafi kimanin naira biliyan 75 wanda za a taimakawa matasa daga shekaru 18 zuwa 35,

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare ya bayyana cewa gwamnatin tarayya da majalisa sun amince domin fara ba da wannan tallafi ga matasa domin inganta sana'o'i, ya kara da cewa, yana ganin wannan shi ne tsarin taimako na farko da aka taba yi a Najeriya,

A wani bincike da jaridartalaka.com.ng ta gudanar, ta gano cewa, akwai wadansu abubuwa guda goma (10) da kowane matashi ya kamata ya sani kafin a fara,

Jawabin wadannan abubuwa guda 10 ya fito ne daga hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad, inda yake cewa ya kamata kowane matashi ya yi kokari ya san su.

Daga cikin abubuwan guda 10:

1. A ranar laraba 22 ga Yuli ne gwamnatin tarayya ta amince da wannan kudurin domin tallafawa matasa masu karamin karfi, sunan shirin NYIP,


2. Sannan kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, duk shekara za a yi amfani da kimanin naira biliyan 25, idan aka samu shekara uku, kudin zai kai kimanin naira biliyan 75 jimulla, sannan za a soma a cikin wannan shekara 2020 inda za a yi amfani da kimanin naira biliyan 12.5,

Sannan kuma ana fatar sababbin gwamnoni za su cigaba daga inda aka tsaya.

3. Daga dan shekaru 18 zuwa 35, su ne kadai za su iya samun wànnan tallafin

4. NYIP daya ne daga cikin shirye shiryen shugaba Buhari na yunkurin kawadda talauci a Najeriya.

5. Shirin zai fitarda yawan matasa daga cikin talauci, kuma zai basu dama su zamo masu dogaro da kai,

6. Kimanin mutum dubu dari  biyar (500,000) ne za a baiwa wannan tallafin bashi, kuma karancin kudi zai fara ne daga dubu dari biyu da hamsin (250,000) zuwa miliyan hamsin, kuma ma'aikatar matasa tareda babban bankin kasa ne za su tsara yadda za a fara ba da tallafin,

7. Kudin za su fito ne daga kungiyoyin dake bada bashi da suka hada da CBN da kuma BOI,

8. Babban bankin CBN tareda ma'aikatar tsara kasafin kudi ne za su bayarda wannan tallafin,

9. Ma'aikatar matasa da wasanni ce za su tsara yadda za a bada tallafin ta hanyar nada kwamitin amintattu kuma masu kaifin basira.

10. Duk wani kasuwanci da mutum zai kawo ya tabbatar ba shirme bane, sannan dole mutum ya gabatar da wakilansa tareda gabatar da wani muhimmin al'amari a tartare dashi.

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.