Header Ads

Header ADS

Cristiano Ronaldo ya kafa babban tarihi a gasar premier, Laliga da kuma Serie A


Kungiyar kwallon kafa a kasar Italiya wato Juventus sun samu nasarar ba da tazara ga kungiyar da ke biye masu baya a teburin serie A wato Inter Milan, inda Juventus din ta ba da tazarar maki takwas jimulla,

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci (Half Time) fitaccen dan wasan Juventus Cristiano Ronaldo ya kai wani farmaki mai zafi inda kwallon ba ta samu shiga ragar Inter Milan ba amma ta taba hannun dan wasan na Inter Milan, wanda hakan ya janyo bugun daga kai sai mai tsaron gida, (Penalty), kuma Ronaldo shi ne ya buga inda ya jefa kwallon a cikin raga.

Ronaldo dai ya yi ta kai hare hare inda saura kiris yaci kwallonshi ta uku lokacin da ya yi amfani da kai wajen jefa kwallon, to sai dai kwallon ba ta samu shiga ba amma ta bugi  sandar ragar Lazio a lokacin da wasa ta kai mintuna 66,

To sai dai dan wasan Lazio ya jefa kwallo daya a ragar Juventus ana minti 83 da yin wasar, kuma an tashi 2-1 ne tsakanin kungiyoyin biyu, Juventus na da kwallo 2 a raga ya yinda Lazio keda kwallo 1 a raga.

Sakamakon kwallaye biyu da Ronaldo ya zura a wannan wasar, hakan yasa ya zamo dan wasa na farko a duniya da ya fara cin kwallaye 50 a gasar premier league, Laliga da kuma Serie A,

Kuma yanzu haka yana da kwallaye 30 a wannan gasar ta bana, kuma kwallayensa sun yi dai dai da na dan wasan Lazio Ciro Immobile.

Latsa link din dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.