Header Ads

Header ADS

Babu matsalar tsaro a Kaduna yanzu, sai dai matsalar COVID-19


Fitaccen gwamna a Najeriya Malam Nasir El-rufai, gwamnan jihar Kaduna ya buga kirji yana mai cewa, yanzu babu wata matsala mai kama da rashin tsaro a jihar Kaduna, domin tuni ya magance wannan matsala,

Sai dai ya bayyana cewa akwai matsalar cutar nan ta Coronavirus dake yaduwa a duk fadin Najeriya ba wai jihar Kaduna kadai ba, wanda hakan ya sanya dole sai gwamnati ta kafa dokar hana yaduwar cutar,

El-rufai ya kara da cewa, aikin titin nan daga Kaduna zuwa Abuja zai taimakawa harkar tsaro sosai, duk da dai ya bayyana cewa yanzu ya samar da tsaro a jihar, domin rabon da ayi garkuwa da wani a titin Kaduna zuwa Abuja tun watan Octoban bara,

Gwamnan ya ambato wasu dokoki da duk wani matafiyi  dole ne ya kiyaye su idan zai shiga jirgi kamar haka:
'Dole ne matafiyi ya saka takunkumin fuska a lokacin da zai zo filin jirgin', sannan zai bar takunkumin a fuska har zuwa lokacin da zai sauka,

El-rufai ya yi magana akan karin kudi da hukumar jiragen kasa ta yi, ya ce shi a wurinsa wannan ba abin tayar da hankali bane,

Ya bayyana cewa yaso ma a ce kudin sun fi haka, domin akwai wadanda idan suka zo basu samu tikitin ba zasu bi ta bayan fage, wanda hakan ba dai dai bane, amma idan aka kara kudin tafiyar sosai, hakan zai sanya masu irin wannan halin su daina,

Har ila yau, ya kara da cewa, maimakon a ce wasu ne suke harkar tikitin gara a ce gwamnati ce take yi domin za ta kara samun kudin shiga wanda za ta amfana da su,

Ministan sufuri a Najeriya, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa, aikin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki gadan gadan bayan hutun Coronavirus wanda zai kare 29 ga watan Yuli,

Amaechi ya ce an kara kudin kujera ne sakamakon chanja fasalin zama da aka yi domin samun tazara tsakanin al'umma dake zaune a cikin jirgi guda,

Yanzu haka, kujerar da ake biyan naira 1,300 mun kara kudinta zuwa naira 3,000, wadda ake biyan naira 2,500 mun kara kudin ta zuwa naira 6,000.

Source: alummata.com

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇
https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.