Header Ads

Header ADS

Ali Nuhu: Za a daura auren Ali Nuhu gobe talata - karanta a nan


A wani al'amari dake cike da ban mamaki a yau shi ne, idan aka ce maka jarumi Ali Nuhu zai kara aure tabbas zaka yi mamaki, domin mafi yawan mutane sun dauka cewa Ali Nuhu mallakin Maimuna ne kadai ganin yadda suke kaunar juna kuma suke zaune lafiya,

A wani bangare kuma ana ganin kamar jarumi Ali Nuhu bai damu da yin mata fiye da daya ba, to sai dai ana cikin haka, kwatsam sai ga wasu hotunan aure wadanda ango da amarya ke yi kafin zuwan bikin (Pree - Wedding)

Daya daga cikin masu shirya fina-finai a masana'antar Kannywood, kuma na hannun daman jarumi Ali Nuhu, Abubakar Bashir Maishadda, ya wallafa hoton Ali Nuhu tare da amaryarsa Maryam Lamido, inda ya rubuta 28/July ne fa! Ma'ana yana nufin gobe ita ce ranar daurin auren jarumi Ali Nuhu kamar yadda shafin hausaloaded.com ya ruwaito,

Muna rokon Allah Yasa a daura wannan aure lafiya, ya kuma baiwa ango da amarya hakurin zama, ku kasance damu idan akwai wani karin bayani zamu sanarda ku.

Latsa nan domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.