Header Ads

Header ADS

Ali Nuhu: Gaskiyar magana akan sabon auren jarumi Ali Nuhu Mohammed


Assalamu Alaikum warahmatullah!
Masoyan wannan jarida tamu da fatar kuna cikin koshin lafiya, Allah Yasa haka amin.

Kamar dai yadda muka yi muku alkawari a kwanakin baya idan kuna biye damu, mun kawo muku labarin kara aure na fitaccen jarumin fina-finan Hausa a Najeriya da ma na kudancin Najeriya, Ali Nuhu Mohammed,

Idan baku manta ba, mun fada muku cewa ku cigaba da kasancewa tare da mu idan akwai wani karin bayani zamu sanarda Ku, JARIDARTALAKA a kodayaushe tana kokari wajen kawo muku sahihan labarai,

Wanda haka yake nuna cewa, ba zamu taba buga labarin da bashi da asali balle makama ba, a wani bincike da JARIDARTALAKA ta yi, ta gano cewa, jarumi Ali Nuhu ba aure zai kara ba, har yanzu dai yana nan da matarsa daya tilo, wato MAIMUNA MOHAMMED ALI NUHU,

Wadannan hotunan aure da kuke gani suna yawo a ko'ina, (Pree Wedding), hotuna ne a cikin wani sabon shirin film mai suna 'GIDAN BIKI' wanda malam Ibrahim Sharukhan ya dauki nauyin shiryawa,

Idan baku manta ba, ire iren wadannan labarai suna yawan faruwa a tsakanin al'umma, domin ko a kwanakin baya an samu irin wannan labari marar asali, tsakanin jaruman Kannywood 'Saddiq Sani Saddiq' da jaruma 'Rahama Sadau' in da aka yi ta tsegumin cewa aure zasu yi a tsakanin su bayan auren a cikin wani shirin film ne kawai,

Jarumi SANI MUSA DANJA, shima ya hadu da irin wannan kalubale a cikin wani shirin film da ya fito na kudancin Najeriya (Nollywood)

Ku kasance da JARIDARTALAKA domin samun ingantattun labarai a kodayaushe, sai dai babu hanzari a cikin labaran da muke wallafawa zuwa gareku, domin sai mun bi diddigin labari kafin mu buga shi zuwa gare ku.

Latsa rubutun dake kasa domin shiga group dinmu na WhatsApp:👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/IBBQQT3lmuAB23LAz6iGS9

No comments

Powered by Blogger.